Home Labaru Almundahana: Hukumar EFCC Ta Kammala Shirin Gurfanar Da Ma’aikaciyar JAMB

Almundahana: Hukumar EFCC Ta Kammala Shirin Gurfanar Da Ma’aikaciyar JAMB

345
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (EFCC) za ta gurfanar da ma’aikaciyar hukumar JAMB, Philomina Chishe, tare da wasu mutane biyar akan badakalar naira miliyan 35.

Rahotanni sun bayyana cewar Chishe ta sanar da hukumar EFCC cewar maciji ne ya hadiye kudin da ake zarginsu da sacewa.

Sauran mutane biyar da za a gurfanar da sun hada da Samuel Umoru da Yakubu Jekada da Daniel Agbo da Priscilla Ogunsola da Aliyu Yakubu.

Wani bangare daga cikin takardar shigar da karar ya bayyana cewar Philomena, wacce ta kasance ma’aikaciyar hukumar JAMB a jihar Benue, ta yi suna bayan ta yi wani kalamai ma su ban mamaki akan cewar wani shu’umin maciji ne ya hadiye naira miliyan 35, da hukumar ta tattara daga sayar da katin rijista a jihar.

A binciken kwakwaf da hukumar EFCC ta gudanar, ta ce ta gano cewar an samu gibin naira biliyan 8 da milliyan 7 kudaden da JAMB ta tattara daga sayar da katin rijista.