Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Almundahana: EFCC Ta Samu Ikon Rufe Asusun Banki Na Jihar Bauchi

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja, ta ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ikon rufe asusun gwamnatin jihar Bauchi na bankin FCMB, domin binciken wata badakalar kudi da ake zargin an tafka ta asusun jihar.

A cikin wata takardar umarni da ta karbo daga kotun tarayya da ke Abuja, hukumar EFCC ta samu izinin rufe asusun gwamnatin jihar har zuwa lokacin da za ta kammala bincike.

Lauyan hukumar EFCC Abubakar Aliyu, ya ce an yi amfani da wasu kamfanonin bogi ne wajen fitar da kudade daga asusun.

Hukumar EFCC dai ta gano cewa, tsohon gwamnan jihar Bauchi Mohammaed Abubakar ne ya yi amfani da kamfanonin wajen fitar da kudaden.

Lauyan na EFCC ya shaida wa kotun cewa, an yi amfani da wasu takardun biyan kudi wajen fitar da naira biliyan 19 da miliyan 8 daga asusun gwamnatin jihar Bauchi zuwa wasu kamfanonin bogi ana jajibirin mika mulki ga sabuwar gwamnati.

Da alkalin ya tambayi hukumar EFCC ko hakan ba zai shafi ayyukan gwamnatin jihar ba, lauyan ya ce ko kadan hakan ba zai shafi jihar ba, saboda ba shi ne wanda jihar ta ke karbar kason ta daga asusun tarayya ba. �

Exit mobile version