Hukumar EFCC ta musanta kama tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, biyo bayan mika karagar mulki ga sabon gwamnan jihar, Emeka Ihedioha.
Labarin kama tsohon gwamnan dai ya yi ta yawo a kafafen yada labarai na zamani, cewa hukumar EFCC ta kama Okorocha.
Mai rikon mukamin shugaban sashen yada labarai na hukumar, Tony Orilade, ne ya karyata labarin, inda ya kara da cewar ba aikin su bane bincikar labaran boge, amma aikin hukumar EFCC shi ne binciken kudaden cin hanci da kuma rashawa.