Home Labaru Almundahana: EFCC Ta Kwace Wasu Gidajen Saraki A Legas

Almundahana: EFCC Ta Kwace Wasu Gidajen Saraki A Legas

612
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kwace wasu gidaje mallakar shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

Hukumar EFCC ta ce gidajen da aka kwace sun hada da  mai lamba 15a, 15b da 17 dake kan titin Macdonald a unguwar Ikoyi na jihar Legas.

Idan dai za a iya tunawa Bukola Saraki ya ambaci gida mai lamba 15 a matsayin mallakin sa a cikin fom din da ya bayyana kadarori, saboda haka hukumar EFCC na zargin cewar ya sayi gidajen ne ta hannun kamfanin man fetur na Shell a karkashin shirin fadar shugaban kasa na sayar da kadarorin gwamnati.

Wani na hannun damar Saraki, da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce hukumar EFCC ta garkame gidaje, saboda ta dade da fara bincike a kan kadarori da kudaden da Saraki ya mallaka.Sai dai an gano cewar hukumar EFCC ba ta iya tantance takamaiman gidajen Saraki ba, lamarin da ya sa hukumar ta sa musu jan fenti tare da makala takardu a  dukkanin su.

Leave a Reply