Home Labaru Almundahana: EFCC Ta Kama Wani Matashi A Legas

Almundahana: EFCC Ta Kama Wani Matashi A Legas

472
0

Ofishin hukamar EFCC reshen jihar Legas ya kama matashi mai shekaru 26, Olalegbin Christopher bisa zarginsa da almundahanar kudaden da yawansu ya kai miliyan N22.

A ranar Alhamis 19 ga watan Satumba ne aka gurfanar da Christopher a gaban kotu tare da kamfanoninsa guda biyu na Pentview Luxury Real Estate Management Limited da Gelbin Technology Limited.

Jastis Oluwatoyin Taiwo na kotun laifuka na musamman dake Ikeja ne ya saurari karar. A wani zancen da hukumar yaki da cin-hancin ta fitar ya na cewa, an gurfanar da wanda ake zargin ne bisa tuhumarsa da aikata laifuka guda biyu, na daya kuwa shi ne almundahana.

EFCC ta kama wani matashin bisa almundahanar miliyan N22.2 tare da taimakon FBI (Hoto) Source: Facebook Rahotanni daga manema labarai sun tabbatar man da cewa an samu kama Christopher a sakamakon wani samamen hadin gwiwa tsakanin EFCC da hukamar FBI kasancewarsa yana ta’ammuli da yanar gizo wurin yin damfara da satar kudade.

Abu na biyu da ake zargin Christopher da aikatawa shi ne, amfani da kamfaninsa da yake yi domin cigaban miyagun ayyukansa.

A cikin takardar da hukumar EFCC ta rubuta domin shigar da karar Chistopher ta fadi cewa, a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 wannan mutum ya mallaki kudi naira miliyan 22 ta hanyar damfara kawai wadda akasari yake yin amfani da yanar gizo.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, wanda ake tuhumar sam yaki amincewa da laifinsa. M.K. Bashir wanda shi ne ya shigar da wannan kara ya roki kotu da ta kara masa lokaci domin gabatar da shaidu gameda wannan kara.

Kuma ya nemi alkalin kotu da ya bada umarnin a cigaba da tsare Christopher har zuwa lokacin da shari’ar za ta kammala, a takaice dai kada a bayar da belin mutumin.

Leave a Reply