Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Almudahanar N2.1bn: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Hukuncin Da Aka Yanke Wa Maina

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta tabbatar da hukuncin
ɗaurin shekaru takwas da aka yanke wa tsohon Shugaban
Kwamitin Kula da Fansho Abdulrasheed Maina bisa yin
sama-da-faɗi da kuɗaɗen fansho Naira biliyan 2 da miliyan
100.

Alƙala uku da su ka saurari shari’ar baki ɗaya sun yi ittifaƙi a kan tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina kamar yadda Mai Shari’a Okon Abang ya karanto.

Jagoran alƙalan mai shari Elfreda Williams-Daudu, ya tabbatar da hukuncin da Babbar Kotu ta yanke wa Maina, wanda a kan haka ne ya ɗaukaka ƙara.

Alƙalin ya ce an yi wa Maina adalci wajen sauraren shari’ar, domin mai tuhuma ya gabatar da hujjoji gamsassu.

Exit mobile version