Gwamnatin tarayya ta ce ta na shirin hana almajiranci a Nijeriya musamman a yankin arewaci.
Mai ba shugaban kasa Buhari shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguna ya bayyana haka, inda ya kara da cewa, akwai wasu kungiyoyin da za a haramta ayyukan su a Nijeriya.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Babagana Munguno ya tabbatarwa ‘yan jaridu haka ne jim kadan bayan kammla wani taro da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a Abuja.
Babagana ya ce duk da cewa, ilimin yara na da muhimmanci, rashin aikin yi da talauci da yawaitan haihuwa na daga cikin abubuwan da ke kara janyo tabarbarewar tsaro a Nijeriya. A karshe ya ce gwamnatin tarayya ta ware kimanin dala biliyan 1 domin inganta harkokin tsaro a Nijeriya.