Home Labaru Almajiranci: Akwai Kimanin Muna Almajirai Miliyan Biyu A Jihar Zamfara

Almajiranci: Akwai Kimanin Muna Almajirai Miliyan Biyu A Jihar Zamfara

435
0
Almajiranci: Akwai Kimanin Muna Almajirai Miliyan Biyu A Jihar Zamfara
Almajiranci: Akwai Kimanin Muna Almajirai Miliyan Biyu A Jihar Zamfara

Direktan kasafin Kudi na jihar Zamfara Hamza Salisu ya ce akwai kimanin almajirai miliyan biyu da ke yawo a kan titunan jihar.

Salisu ya bayyana haka ne a lokacin wani taro a kan kare hakkin yara da cigaban su wanda kungiyar Save the Children International ta shirya a garin Gusau.

Hamza Salisu ya ce, alkalumman da ke hannun su sun nuna cewa, akwai kimanin almajirai miliyan biyu a jihar, wanda hakan ba karamin barazana ba ne ga cigaban jihar.

Haka kuma, Salisu ya ce gwamnati na da ikon bullo da tsare-tsare domin magance matsalar almajiranci, amma akwai rawar kungiyoyi da dai-dai-kun mutane da za takawa a kan lamarin.

Daraktan ya kuma yi kira ga iyaye su tabbatar sun sauke nauyin kula da ‘ya’yan su domin rage kallubalen da ake fama da shi a cikin al’umma.

A nashi bangaran, daraktan harkokin shari’a na jihar Nasiru Jangebe ya dora laifi a kan wasu malamai da ke yi wa ayoyin al’ukr’ani fasara bisa kuskure domin halasta bara a cikin al’umma.