Home Labaru Al’kalumma: Nijeriya Na Fitar Da Gangar Mai Fiye Da Miliyan 2 A...

Al’kalumma: Nijeriya Na Fitar Da Gangar Mai Fiye Da Miliyan 2 A Duk Rana

287
0
Satar Mai: Nijeriya Ta Yi Asarar Bilyan 17 Cikin Watanni 5 – NNPC
Satar Mai: Nijeriya Ta Yi Asarar Bilyan 17 Cikin Watanni 5 – NNPC

Kamfanin matatar man fetir na kasa NNPC ya sanar da cewa, Nijeriya na fitar da gangan danyen mai miliyan biyu da dubu goma sha tara, a duk rana.

shugaban kamfanin Maikanti Baru ya bayyana haka a lokacin taron kasa da kasa a kan harkokin tama karo na 12 da ya gudana a Abuja.

Maikanti Baru ya ce, tun bayan darewar sa shugabancin kamfanin na NNPC, an samu cigaba na adadin danyen man da ake fitarwa a Nijeriya daga ganga miliyan 1 da dubu rai 8 da 6 a shekara ta 2017 zuwa 2019 da kuma 2018, wanda hakan ke nuna cewa, an samun karuwar fiye da kashi 9.

Shugaban ya kara da cewa, an samu yawaitan man fetir a Nijeriya a ‘yan shekarun nan fiye da shekarun baya, inda ya ce a shekara ta 2018 sun siyar da litar man fetur biliyan 1 da miliyan dari 2, ba kamar a shekara ta 2017 da aka siyar da litan biliyan 1 da miliyan dari ba.

Haka huma Maikanti Baru ya bayyana ma mahalarta taron cewa, kamfanin NNPC ya samu gagarumar nasara a kokarin da yak e yi na hakar man fetur a wurare da dama a Nijeriya, musamma na tafkin Kolmani, inda aka haka fiye da zurfin kafa dubu goma.

Leave a Reply