Home Home Alhini: Tinubu Ya Soke Bikin Haihuwar Sa Saboda Harin Jirgin Kaduna

Alhini: Tinubu Ya Soke Bikin Haihuwar Sa Saboda Harin Jirgin Kaduna

212
0
Jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya soke taron bikin cika shekaru 70 da haihuwar sa, wanda aka shirya gudanarwa a birnin Lagos saboda nuna alhini ga mutanen da su ka jikkata da wadanda su ka rasa rayukan su sakamakon harin jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Duk da cikar da dakin taron ya yi a Lagos, Tinubu ya bukaci limaman addini da mahalarta taron su yi addu’a ga wadanda hadarin ya ritsa da su, a kuma yi wa Nijeriya addu’a domin samun nasarar yakin da ta ke yi da ‘yan ta’adda.

Tinubu ya ce a matsayin sa na daya daga cikin dattawan kasa, bai dace a ce ya na gudanar da bukukuwa a daidai lokacin da wasu ke juyayin rashin ‘yan’uwan su ko kuma samun raunukan da su ka yi ba.

Hakan ya sa tsohon gwamnan ya sanar da soke bukukuwa nan take, inda ya bukaci kowa ya koma gidan sa bayan ya yi wa jama’a godiya.

Leave a Reply