Home Labaru Kiwon Lafiya Alhini: Dan Sheikh Muhammed Auwal Aya Ya Rasu A Sanadiyyar fadawa Ruwa

Alhini: Dan Sheikh Muhammed Auwal Aya Ya Rasu A Sanadiyyar fadawa Ruwa

272
0

Mun samu labarain rasuwar wani matashi mai suna AbulFadal
Abbas Muhammed wanda ke zama da ga Sheikh Muhammed
Auwal AYA wani fitaccen malamin addinin musulunci dake
zaune a Kudundumau a gundumar Asokoro a nan birnin Abuja,


Marigayi AbulFadal Abbas Muhammed mai shekaru 15 ya rasu ne a sanadiyyar fadawa da yayi a kogi a garin Gwantu dake karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna,


An gunanar da janaizarsa tare da binne shi a makabartar Zange dake garin na Gwantu,


Daga bisani aga gudanar a Addu’oin kwanaki bakwai na rasuwarsa a unguwar Kudundumau inda mahaifinsa ke zaune Dafatan Allah SWT ya jikansa da rahma yasa jannatul firdauci ce makomarsa mu kuma idan tame ta zo allah yasa mu yi kyakkawan karshe.

Leave a Reply