Home Labarai Alhani: Sarkin Kano Na 14 Ya Bayyana Kyakykyawar Alakar Dake Tasanin Sa...

Alhani: Sarkin Kano Na 14 Ya Bayyana Kyakykyawar Alakar Dake Tasanin Sa Da Herbert Wigwe

102
0

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmowa a lokacin da aka sauke shi daga karagar sarautar Kano.

Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami’in bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalin sa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwar sa.

Ya ce tsohon jami’an bankin na Acces ya yi masa alƙawarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.

Tsohon gwamnan na CBN ya ce a lokacin har jirgin sama marigayi Herbert Wigwe ya tanadar masa don ɗaukar sa daga Kano zuwa Legas.

Leave a Reply