Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Alhani: Sarkin Kano Na 14 Ya Bayyana Kyakykyawar Alakar Dake Tasanin Sa Da Herbert Wigwe

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmowa a lokacin da aka sauke shi daga karagar sarautar Kano.

Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami’in bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalin sa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwar sa.

Ya ce tsohon jami’an bankin na Acces ya yi masa alƙawarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.

Tsohon gwamnan na CBN ya ce a lokacin har jirgin sama marigayi Herbert Wigwe ya tanadar masa don ɗaukar sa daga Kano zuwa Legas.

Exit mobile version