Ministan kwadago Chris Ngige, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fara biyan kananan ma’aikata mafi karancin albashi na naira dubu talatin.
Yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a Enugu, Ngige, ya yi watsi da ikirarin kungiyar kwadago cewa gwamnatin tarayya ba ta da niyyar fara biyan albashin.
Ya ce kaddamar da sabon tsarin fara biyan mafi karancin albashin ma’aikatan babban kalubale ne da ba zai tabbata a lokaci guda ba.
Ministan ya cigaba da cewa, ya zuwa yanzu sabon tsarin ya fara tasiri a kan kananan ma’aikatan gwamnatin tarayya daga kan mataki na daya zuwa na shida. Sai dai ya ce babu karin albashin ba zai takaita kawai a kan kananan ma’aikata ba, domin zai yadu har zuwa ga manya, lamarin da ya ce ba zai yiwu kananan ma’aikata da manya su rika daukar albashi kai daya.
You must log in to post a comment.