Home Labaru Kasuwanci Albashi: Za A Hukunta Ma’aikatu Masu Zaman Kan Su Da Basu Biyan...

Albashi: Za A Hukunta Ma’aikatu Masu Zaman Kan Su Da Basu Biyan Dubu 70

40
0
1x 1
1x 1

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga kamfanoni masu zaman kan su su bi tsarin mafi ƙarancin albashi na N70,000, inda ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da saɓanin yin hakan ba.

A cewar Gwamnatin, sabon mafi ƙarancin albashi ya zama dole don magance yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu.

Ta jaddada cewa babu wani ma’aikacin Najeriya, ko yana aikin gwamnati ko na kamfani mai zaman kan sa da za a biya ƙasa da mafi ƙarancin albashin na Naira 70,000.

Babban sakataren Ma’aikatar Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi ta Tarayya Ismaila Abubakar, ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na ƙungiyar ma’aikatan kamfanoni masu zaman kan su na Najeriya karo na 13, wanda aka gudanar a Ikeja, ta jihar Legas.

Isma’il Abubakar wanda Daraktan Ɗaukar Ma’aikata da Albashi na ma’aikatar, John Nyamali, ya wakilta ya ce, a yanzu mafi ƙarancin albashi ya zama doka,

saboda haka laifi ne da ke da hukunci ga duk wani mai ɗaukar ma’aikaci ya biya ƙasa da N70,000 ga kowane ma’aikacin sa.

Ya ce kamfanoni masu zaman kan su su san hakan ya zama wajibi a duk wata kwangila da za su karɓa daga hannun masu ɗaukar aiki cewa kada ma’aikatan su su riƙa samun ƙasa da mafi ƙarancin albashi.

Ya kara da cewa mafi ƙarancin albashi ga ma’aikaci a Najeriya shi ne N70,000, kuma yana ganin ya kamata ya samu hakan bayan an cire adadin da za zaftare.

Leave a Reply