Gwamnatin Tarayya ta ce mutum 123,000 ne ke cin moriyar shirin bayar da tallafin Shugaba Buhari a yankin Kudu maso Kudu, wato Neja Delta.
Minista a Ma’aikatar Kudi da Kasafi da Tsare-tsaren Kasa, Prince Clems Agba, ya ce an zabo masu amfana da tallafin ne daga kananan hukumomin yankin 123 karkashin shirin daukar kananan ma’aikatan wucin gadi 1,000 a kowace karamar hukuma.
Da yake bayani gabanin tattaunawar sa da masu cin gajiyar shirin, Prince Clems ya ce, Shirin na daga cikin yunkurin Shugaba Muhammadu Buhari na rage wa ‘yan Najeriya radadin illar COVID-19 ga tattalin arzikin su kamar yadda bullar annobar ta girgiza tattalin arzikin gwamnatoci da kamfanoni da daidaikun mutane a fadin duniya.
Ministan ya ce a karkashin shirin da Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa NDE take gudanarwa, ana biyan kowane mutum Naira 20,000 a duk wata.
Idan aka ninka yawan kananan hukumomin yankin Neja Delta da mutum 1,000 da suka ci gajiyar wannan shiri, za a samu mutum 123,000, baya ga Naira biliyan daya da Gwamnatin Tarayya ta ware wa yankin Kudu maso Kudu na gyaran hanyoyi.