Home Labaru Agaji: Saraki Ya Sadaukar Da Kudinsa Ga Iyayen Leah Sharibu Da Wasu...

Agaji: Saraki Ya Sadaukar Da Kudinsa Ga Iyayen Leah Sharibu Da Wasu Mutane 3

519
0
Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Bukola Saraki, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya sadaukar da kudin da zai samu na barin majalisa ga iyayen wasu mata uku da ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram su ka shafa.

Saraki ya bayyana haka ne ta bakin Kakakinsa Yusuph Olaniyonu, inda ya ce baya ga matan guda uku, Saraki ya sadaukar da sauran kudin ga iyalan takwarorin sa Sanatoci da su ka mutu domin amfanin abin da su ka bari.

Wadanda za su amfana da kudaden kuma sun hada da iyayen dalibar da Boko Haram ta sace daga makarantar ‘yan mata da ke garin Dapchi a jihar Yobe Leah Sharibu, sai kuma iyayen Hussaina Ahmed da Hauwa Liman, da jami’an bada agaji da Boko Haram su ka kashe.Bukola Saraki ya sadaukar da kashi 20 cikin 100 na kudin ga iyayen Leah Sharibu, da kashi 20 ga iyayen Hauwa Liman, da kashi 20 ga iyayen Hussani, sai kuma sauran kaso 40 da za a yi amfani da shi wajen kafa gidauniyar da za ta taimaka wa iyalan Sanatocin da su ka mutu idan har bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply