Afirka ta Kudu ta yi maraba da batun tsagaita wuta da
kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a
gaggauta a Gaza.
A cikin wata kuri’a da a ka kada a jiya Litinin, kwamitin ya bukaci a tsagaita wuta har zuwa karshen watan Ramadan, wanda zai kare nan da makonni biyu.
Cikin wata sanarwa da ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandorin, ta fitar ta ce, kasarta ta ji dadin yarjejeniya, sai dai ta yi kira da a samu tsagaita wuta ta dindindin.
Ta ce kara da cewa, yanzu alhakin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin duniyar ne ya tabbatar da cewa ba a samu wata matsala a wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta ba.
Yarjejeniyar tsagaita wutar wadda a cikinta a ka yi kiran da a saki mutanen da a ka tsare da su, ta samu cikas a lokuta da dama. Wannan ne dai karon farko da kwamitin ya yi wannan kiran tun bayan fara yakin.