Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Afghanistan: Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen duniya su hada kai wajen murkushe barazanar ayyukan ta’addancin dake tasowa daga Afghanistan sakamakon karbe ikon da kungiyar Taliban tayi a kasar.

Yayin da yake tsokaci a taron gaggawa na kwamitin sulhu, Guterres, yace ya zama wajibi duniya ta hada kai wajen hana Afghanistan zama dandalin aikata laifuffuka da kuma ba ‘Yan ta’adda mafaka.

Sakataren ya roki kwamitin sulhu da kasashen duniya gaba daya suka hada kai wajen aiki tare wajen dakushe barazanar tsaron dake fitowa daga Afghanistan da kuma tabbatar da mutunta ‘yancin Bil Adama a kasar.

Jawabin Guterres na zuwa ne bayan da mayakan Taliban ke ci gaba da shawagi a titunan birnin Kabul sakamakon nasarar da suka samu na karbe iko da kasar bayan shekaru 20.

Rahotanni sun ce dubban mutane ne suka mamaye tashar jiragen saman birnin Kabul inda manyan kasashen duniya suka aike da jirage domin kwashe ‘yan kasashen su domin barin kasar.

Sakatare Janar din yace kwanaki masu zuwa nan gaba na da matukar tasiri dangane da makomar kasar, yayin da kasashen duniya zasu zuba ido domin ganin abinda zai faru a kasar, inda yake cewa mutanen Afghanistan na bukatar taimako, kuma bai dace a juya musu baya ba.

Exit mobile version