Home Home Afenifere Ta Yi Alla-Wadai Da Zaɓen Tinubu

Afenifere Ta Yi Alla-Wadai Da Zaɓen Tinubu

30
0
Shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Pa Ayo Adebanjo, ya maida martani a kan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Pa Ayo Adebanjo, ya maida martani a kan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Yayin da ya ke jawabi a wata tattaunawa ta wayar tarho da kafar yada labarai ta BBC, Adebanjo ya bayyana zaɓen da ya ba Tinubu nasara a matsayin mai cike da kurakurai.

Ya ce sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma hakan na iya haifar rikici a Nijeriya.

Adebanjo, ya ce gazawar da hukumar zabe ta yi wajen amfani da na’urar BVAS a rumfunan zaɓe kamar yadda ta yi alkawari tun farko, ya nuna cewa wasu sun tsara yadda zaɓen zai gudana da kuma ɗan takarar da su ke so ya yi nasara.