Home Labaru Ilimi Addu’o’In Zaman Lafiya: Malamin Darikar Tijjaniya Ya Ja Hankalin Al’ummar Musulmi

Addu’o’In Zaman Lafiya: Malamin Darikar Tijjaniya Ya Ja Hankalin Al’ummar Musulmi

181
0

Mayakan kungiyar ISWAP 104 da suka mika wuya sun ce uwar bari suka gani a sakamakon ragargazar da sojoji ke musu ta sama da kasa. Karin mayakan kungiyar ta’addancin da suka mika wuya sun bayyana cewa yin hakan ya zame musu dole ne saboda ragarzazar da jiragen yaki da sojojin kasa suke wa maboyarsu.

Mayakan sun bayyana haka ne bayan sun mika wuya tare da iyalansu a ranar Litinin ga rundunar sojoji ta musamman da ke Damboa Jihar Borno.

Hukumomin sojin Najeriya sun bayyana cewa mutanen da suka mika wuya sun hada da maza 22, mata 27 da kuma kamanan yara.

A baya-bayan nan, shugabannin soji da na siyasa sun karkatar da hankulansu zuwa yankin Kudancin Borno, a sakamakon yawan hare-haren ta’addancin da ISWAP ke kaiwa a yankin da ya hada da Damboa, Chibok, Askira Uba da sauran wuraren da ke makwabtaka da Tabkin Chadi.

Majiyoyi masu tushe sun shaida wa manema labarai cewa mayakan na samun sauki kurdawa su koma Dajin Sambisa da Dajin Alagarno bayan sun kai hare-hare a kananan hukumomin da aka ambata.

Idan ba a manta ba a yankin Askira Uba ne mayakan ISWAP suka kai wa ayarin motocin Kwamandan Birged na Musamman na 28, Birgediya Dzarma Zirkushu, suka kashe shi da wasu sojoji uku a watan Nuwamban 2021.

Leave a Reply