Home Labaru Adawa: PDP Ta Bukaci Buhari Ya Tanadi Shedar Kammala Sakandare Don Kare...

Adawa: PDP Ta Bukaci Buhari Ya Tanadi Shedar Kammala Sakandare Don Kare Kanshi A Kotu

212
0

Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tanadi takardun sa na kammala makarantar sakandare domin kare kan sa a kotu.

PDP ta bayyana haka ne bayan wata sanarwar da mai magana yawun shugaban kasar Festus Keyamo ya fitar a gidan talabijin na Channels, inda ya ke nuna cewa ba dole ba ne sai mutum ya na da takardun kammala sakandare zai iya yin shigabanci kasa ko gwamna a Nijeriya ba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar, PDP ta bukaci ‘yan Nijeriya su lura da maganar da Keyamo ya yi na cewa, ba dole sai mutum ya na da takardun sakandare zai iya yin mulki a Nijeriya ba, mutukar zai iya magana da harshen turanci, wanda a cewar sa hakan ya na nuni cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da takardun sakandare kenan.