Home Labaru Acaba: Gwamnatin Legas Ta Haramta Baburan Okada Da Keke Napep

Acaba: Gwamnatin Legas Ta Haramta Baburan Okada Da Keke Napep

1427
0
Acaba: Gwamnatin Legas Ta Haramta Baburan Okada Da Keke Napep
Acaba: Gwamnatin Legas Ta Haramta Baburan Okada Da Keke Napep

Gwamnatin jihar Legas, ta haramta baburan haya da aka fi sani da Okada da kuma Keke Napep a wasu kananan hukumomi da gadoji da kuma manyan hanyoyin da ke jihar.

A cikin wata sanarwar da mai ba Gwamna Babajide shawara ta fuskar yada labarai Jubril Gawat ya fitar, ta ce haramcin hayar ya shafi baburan kamfanonin sufuri na Opay da kuma Gokada.

Sanarwar ta kara da cewa, dokar haramta hayar baburan za ta soma aiki ne daga ranar 1 ga watan Fabarairu na shekara ta 2020.

Daga cikin kananan hukumomi da manyan yankunan da dokar ta shafa akwai Apapa, da Apapa Iganmu, da Lagos Mainland, da Yaba, da Surulere, da Itire Ikate, da Coker, da kuma Aguda.

Sauran yankunan sun hada da Lagos Island, da Ikeja, da Eti-Osa, da Ikoyi da Obalende, da Lagos Island ta gabas, da Ojodu, da Onigbongo da kuma Iru Ikoyi zuwa Obalende.

Leave a Reply