Home Labaru Abubuwan Da Na Gaya Wa Shugaba Tinubu – Muhammadu Sanusi II

Abubuwan Da Na Gaya Wa Shugaba Tinubu – Muhammadu Sanusi II

100
0

Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya bayyana abin da ya
tattauna da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan ya kai
ma shi ziyara a fadar sa da ke Abuja.

Basaraken, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya ne, ya ce yayin ganarwar ya gode wa shugaba Tinubu dangane da alkiblar da ya dauka a kan gyara tattalin arzikin Nijeriya ciki kuwa har da cire tallafin man fetur da samar da farashin musayar dalar Amurka da sauran su.

Yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Basaraken ya ce wadannan abubuwa ne da ya dade ya na magana a kan su, kuma ya yi farin cikin yadda Tinubu ya fara magance su a ranar farko ta kama aikin sa.

Muhammadu Sanusi II dai ya gana da shugaba Tinubu ne kwanaki kadan bayan an cire Godwin Emefiele daga mukamin sa tare da kaddamar da bincike a kan ofishin sa.

Ya ce ya ba Tinubu shawara a kan matakan da su ka kamata a fara dauka domin magance matsalar tsaro, amma abu mafi muhimmanci shi ne, ya yi ma shi maganar makiyaya 37 da aka kashe a jihar Nasarawa watannin da su ka gabata.

Leave a Reply