Daya daga cikin ’yan makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya dake Birnin Yauri a jihar Kebbi, wacce ’yan bindiga suka sace a 2021 ta haihu a hannun wadanda suka sace su.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa dalibar mai shekara 16 na daya daga cikin ’yan mata 11 da har yanzu ba a sako su ba tun bayan sace sama da su 100 da malaman su takwas, a ranar 17 ga watan Yunin 2021.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa kafar cewa dalibar, wacce har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a kai ga tantance sunanta ba, ta haifi da namiji ne a sansanin ’yan bindigar.
Majiyar ta shaida cewa iyayen yaran na cike da damuwa kasancewar har yanzu an ki sakin ’ya’yan na su, duk kuwa da biyan kudin fansa da musayar fursunonin da aka yi da ’yan ta’addan.