Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana dalilin da ya sa bai kara aure ba tun bayan rasuwar tsohuwar matar sa marigayiya Maryam Babangida a watan Disamba na shekara ta 2009.
Yayin wata tattaunawa da manema labarai, Janar Babangida ya ce ya zaɓi yin haka ne domin ya martaba tsohuwar matar shi.
Kwanan baya dai an yi ta raɗe-raɗin cewa, tsohon shugaban kasar ya na shirin yin wani auren don samun abokiyar zama, amma ya ce rahotannin ba gaskiya ba ne.

