Home Labaru Abin Da Jam’iyyu Suka Kashe A Zaben 2019

Abin Da Jam’iyyu Suka Kashe A Zaben 2019

353
0
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta kasa, INEC

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce har zuwa yau jam’iyya daya ce tal ta mika wa masu bayanan yadda ta kashe kudade a wajen yakin neman zaben shekara ta 2019.

Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce duk da doka ta jaddada cewa dole kowace jam’iyya ta bayyana wa hukumar zabe yadda ta samu kudaden ta da yadda ta kashe, amma har yau jam’iyya daya ce kadai ta bi wannan umarni, watanni uku bayan kammala zabubbukan.

Ya ce dokar mai karfi ce a cikin Dokokin Zabe, amma abin takaici babu wata jam’iyyar da ta cika sharuddan ta doka, wadda ta tilasta wa jam’iyyu sanar da hukumar zabe yadda su ka samu kudaden gudummawa daga daidaikun jama’a ko kungiyoyi domin gudanar da yakin neman zabe. A karshe ya ce dokar Zabe ta shekara ta 2010 da aka yi wa kwaskwarima, ta bukaci dukkan jam’iyyu su mika wa hukumar zabe kwafe biyu na bayanan kudaden da su ka kashe a lokacin yakin neman zabe.