Home Home Abin Alfahari: Shugaba Buhari Ya Taya ‘Yan Najeriya Da Suka Lashe Zabe...

Abin Alfahari: Shugaba Buhari Ya Taya ‘Yan Najeriya Da Suka Lashe Zabe a Amurka Murna

187
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika sakon taya murna ga ‘yan asalin Najeriya mazauna Amurka su takwas da suka samu nasarar lashe kujeru daban-daban a zaben rabin wa’adi da aka gudanar a Amurkan.

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasan shawara kan kafofin yada labarai Femi Adesina ya fitar, Shugaba Buhari ya yi musu fatan alkairi a tsawon lokacin mulkin su.

Sannan kuma shugaban kasa ya gode musu bisa taimakekeniya da hadin kai da suke nuna wa junan su a tsawon shekarun da suka kwashe a kasar Amurka.

A jihar Georgia dai mutum biyar ne ‘yan asalin Najeriya suka lashe kujerun majalisar dokokin jihar a gundumomin da suke zaune.

Sannan kuma mutum biyu suka lashe kujerun majalisa a jihohin Pennsylvania da Minnesota.

Haka kuma an sake zabar Dakta Oye Owolewa a kujerar majalisar wakilan Amurkan daga birnin Washington D.C.

Leave a Reply