Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Abdullahi Adamu Ya Sasanta Yari Da Matawalle

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu, ya sasanta tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari da gwamna mai ci Bello Matawalle.

Yayin wani zama da aka yi a Abuja, jiga-jigan jam’iyyar
biyu sun tattauna a tsakanin su, sannan ya shiga tsakanin
su ya sasanta su.

Idan dai ba a manta ba, shugaban Jam’iyyar PDP na jihar
Zamfara ya sanar wa manema labarai cewa Abdul-Aziz
Yari da mukarraban sa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar
PDP.

Sai dai bayan nan sanata Kabiru Marafa ya sanar cewa an
yi riga-malam-masallaci ne, amma har yanzu ba su koma
PDP ba.

Exit mobile version