Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Abduljabbar Kabara: Abin Da Wasiƙar Wasu Iyalan Sheikh Nasiru Ga Buhari Ta Ƙunsa

Wasu daga cikin iyalan shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya ta Afirka Sheikh Nasiru Kabara, sun kai ƙarar wasu malaman jihar Kano wajen Shugaba Muhammadu Buhari a kan lamarin da ya shafi Sheikh Abduljabbar.

Wannan dai ya na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da su ka rubuta wa shugaban ƙasa, mai ɗauke da sa hannun ɗaya daga cikin su Sheikh Sidi Musal Qasuyuni Nasir Kabara.

A cikin wasiƙari, mutanen sun buƙaci shugaba Buhari ya yi ƙoƙarin dakatar da duk wata muzgunawa da rashin adalcin da su ka ce an shirya yi wa ɗan’uwan su.

Sai dai a jerin sunayen wadanda su ka rubuta wasiƙar babu sunan babban ɗan Sheikh Nasiru Kabara, wanda shi ne shugaban Ƙadiriyyar a halin yanzu Sheikh Ƙaribullah Kabara.

Mutanen, sun kuma buƙaci Shugaba Buhari ya sa baki a saki Sheikh Abduljabbar, wanda yanzu haka ke tsare bisa tuhumar sa da yin ɓatanci ga Manzon Allah (S.A.W.).

Exit mobile version