Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, ya kaddamar da tallafin tirela 240 na abincin Azumi ga kananan hukumomi 14 da ke Jihar Zamfara.

Abdulaziz Yari ya kaddamar da bada tallafin abincin ne a Karamar hukumar Talata Mafara, inda ya ce kowacce karamar hukuma za a raba tirela 10, sannan a raba wa ‘yan gudun hijira tirela 13, sauran kungiyoyi kuma tirela 10, yayin da za a raba wa sauran mutanen gari tirela 46.

Zababben Snatan, ya yi kira ga Shugabannin kwamitin rabon kayan azumin su ji tsoran Allah wajen raba kayan abincin, ta yadda kowa zai amfana da shi.

A karshe ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara su kasance masu bin doka da oda.

Exit mobile version