Home Labaru Abbas Ya Sanar Da Manyan Jagororin Majalisar Wakilai

Abbas Ya Sanar Da Manyan Jagororin Majalisar Wakilai

86
0

Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ya sanar da
Julius Ihonvbere daga jihar Edo a matsayin shugaban masu
rinjaye na majalisar, da kuma Usman Kumo daga jihar Gombe
a matsayin mai tsawatarwa na majalisar.

Tajudeen Abbas, ya kuma bayyana Halims Abdulahi daga jihar Kogi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye, da Oriyomi Onanuga daga jihar Ogun a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.

Haka kuma, ya sanar da Kingsley Chinda na jam’iyyaer PDP daga jihar Rivers a matsayin shugaban marasa rinjaye, sai kuma Ali Isah daga jihar Gombe a matsayin bulaliyar marasa rinjaye.

Sauran sun hada daMadaki Aliyu na jam’iyyar NNPP daga jihar Kano a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye, da George Adegeye na jam’iyyar Labour a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Leave a Reply