Home Labaru A Yau Aka Soma Zagaye Na Uku A Najeriya

A Yau Aka Soma Zagaye Na Uku A Najeriya

90
0

A yau Juma’a Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da riga-kafin korona zagaye na uku.

A jiya ne daraktan lafiya a matakin farko na ƙasa, Dakta Faisal Shuaib ya sanar da hakan a sansanin ‘ƴan gudun hijira a nan Abuja.

Dr. Faisal Shuaib ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar amfani da Pfizer Bio-N-tech a zagaye na ukun.

Tuni dai wasu ƙasashen duniya suka soma riga-kafin zagaye na uku domin ƙara ƙarfin riga-kafin a jikin waɗanda aka yi wa zagayen farko da na biyu.