Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara wa jihohi kason kudaden da ake ba su duk karshen wata, domin su fi jin dadin biyan karin albashin ma’aikata cikin sauki.
karanta Wannan: Albashin Hadiman Buhari, Osinbajo Ya Tsaya
Har yanzu dai ana sa-toka-sa-katsi dangane da batun biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankancin albashi.
Masari ya ce, jihar sa ba ta da matsalar kasa biyan karin albashin ma’aikata, domin kowa ya san abin da ta ke samu a kowane wata.
Ya ce gwamnatin jihar Katsina za ta buda yadda tsarin biyan albashin ya ke, sannan ta yi aikin nazarin sa tare da bangaren tsara albashi da kasafin kudaden ayyuka na jihar domin a fara aiki da sabon tsarin.