Home Labaru A Binciki Gobarar ‘Yan Gudun Hijira Da Ke Ngala – Buhari

A Binciki Gobarar ‘Yan Gudun Hijira Da Ke Ngala – Buhari

394
0
Buhari Ya Bukaci A Yi Bincike A Kan Gobarar ‘Yan Gudun Hijira Da Ke Ngala
Buhari Ya Bukaci A Yi Bincike A Kan Gobarar ‘Yan Gudun Hijira Da Ke Ngala

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar kula jin dadin ‘yan gudun hijira da ta gudanar da bincike a kan musabbabin tashin gobara sarsanin ‘yan gudun hijira da a Ngala a jihar Borno.

Gobarar dai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 14, tare da jikkata wasu da dama, matakin da ya sa shugaban kasa Buhari ya bukaci ma’aikatar kula da ‘yan gudun hijira ta binciko makasudin tashin gobarar tare da hanyoyin kauce wa sake faruwar haka a nan gaba.

Kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sa wa hannu ya kuma rabata ga manema labarai.

Shugaba Buhari ya kwatanta gobarar a matsayin wani al’amari mai matukar tada hankali da ban tsoro, saboda haka ya bada umarnin a kai wa wadanda lamarin ya shafa taimakon gaggawa.

Haka kuma, Buhari ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu, tare da fatan samun sauki ga wadanda gobarar ta jikkata.