Home Labaru Aƙalla Haɗarin Mota Na Kashe Rayuka 40,000 Duk Shekara A Nijeriya –...

Aƙalla Haɗarin Mota Na Kashe Rayuka 40,000 Duk Shekara A Nijeriya – Hukumar Kiyaye Haɗurra

100
0

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, ta ce sama da mutane dubu
40 ke mutuwa, yayin da wasu ke samun nakasa sakamakon
haɗurran motoci a Nijeriya duk shekara.

Babban Jami’in hukumar Dauda Biu ya bayyana haka a Abuja, yayin da ya ke jawabi a Makon Kula da Kiyaye Haɗurra na Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 7.

Ya ce yawan waɗannan adadin mace-macen da nakasa duk haɗurran ababen hawa ke haddasa su a Nijeriya.

Dauda Biu ya ƙara da cewa, duk shekara haɗurra su na salwantar da rayuka miliyan 1 d dubu 300 a duniya, sannan fiye da mutane miliyan 50 su na samun raunuka.

Leave a Reply