Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

6 Ga Watan Agusta: Yau Ake Cika Shekaru 75 Da Amirka Ta Kai Hari A Birnin Hiroshima

Shekaru 75 kenan da Amirka ta kai hari da makamin Nukiliya na kare dangi a Hiroshima na kasar Japan, mutum dubu 70 suka rasa rayukansu a yini gudu kafin hari na biyu na Nagasaki da ya lakume dubban rayuka.

A yau shida ga watan Augusta ake cika shekaru sabain da biyar (75) da faruwar harin Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan, Amirka ta soma jefa makamin Nukiliya na kare dangi a birnin Hiroshima kafin ta jefa na biyun a Nagasaki, lamarin da ya sa Japan mika wuya a yayin yakin duniya na biyu.

 Al’umomin a kasar kan hadu a duk rana irinta ta yau don nuna alhini kan iftala’in da yayi sanadiyar rayukan Japanawa kimanin dubu dari da arba’in, amma a bana, annobar Corona ta rage ma taron da ke hada kan ‘yan kasa dama baki daga kasashen duniya armashi.

Firaiminista Shinzo Abe a yayin jawabinsa,  ya ce, kasar za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin an haramta amfani da duk wani na’ui na makamin nokiliya. Tarihi ya nuna cewa, hare-haren na Hiroshima da Nagasaki sun kasance karon farko da ake kai hari da makami mai guba kan bil’adama a duniya.

Exit mobile version