Shugaban rundunar ‘yan Sandan Nijeriya Usman Alƙali Baba, ya ce babu wani gwamna da za a sake bari ya hana jam’iyyun adawa gudanar da taro a jihohin su.
Alkali Baba ya ya bayyana haka ne, a wajen wani taron jam’iyyun siyasa da ya gudana a Abuja, inda ya samu wakilcin Mataimakin Sufeto Janar na Hukumar ‘yan Sanda DIG Dandaura Mustapha.
Ya ce an umarci kwamishinonin jihohi su tabbatar an ba kowane ɓangare damar gudanar da yaƙin neman zaɓe.
Shugaban ‘yan sandan ya ƙara da cewa, yayin da ya kamata a yaba ma wasu gwamnonin da su ka ba jam’iyyun adawa damar gudanar da ayyukan su cikin walwala, akwai kuma ƙorafe-ƙorafe a kan wasu.
Ya ce abin takaici, wasu daga cikin gwamnonin ba su taimaka wa al’amurran wasu jam’iyyu, domin ba su kafa harsashin ba sauran jam’iyyun siyasa damar yin yaƙin neman zaɓe ba. Usman Alkali Baba, ya ce duk kwamishinan ‘yan sandan da bai bi wannan umarnin ba za a sauya ma shi wurin aiki.