Matatar man Ɗangote ta fara fitar da mai daga matatar zuwa ƙasashen Afirka ta yamma masu maƙwabtaka, a wani sabon yanayin kasuwanci da ka iya sauya kasuwar mai a Afirka.
Wani rahoto da mujallar Bloomberg ta fitar ranar Talata inda ta ambato wasu bayanai da aka samu daga Vortexa da Kpler da Priecise Intelligence da ke bin diddigin bayanan jiragen ruwa.
ya ce wani jirgin ruwa ɗauke da mai daga kamfanin Ɗangote ya nufi ƙasar Togo mai maƙwabtaka.
Rahoton ya ce jirgin mai suna CL Jane Austen ya yi lodin mai fiye da ganga 300,000 daga matatar Ɗangoten.
A watan da ya gabata ne dai shugaban kamfanin mai na ƙasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ya ce ƙasar sa na shirin sayen man daga hannun Ɗangote,
Domin taimakon ƙasar rage yawan kuɗaɗen da take kashewa wajen shigar da mai daga nahiyar Turai kimanin dala 400 a kowane wata.