Home Home Ɗan Uwan Ɗan Sanda Ya Kashe Shi Ya Sace Bindigarsa

Ɗan Uwan Ɗan Sanda Ya Kashe Shi Ya Sace Bindigarsa

30
0
Wani jami’in dan sanda da ke gadin wani banki ya gamu da ajalin sa a hannun wani dan’uwan sa, yayin da su ke shirin cin abincin rana a harabar bankin.

Wani jami’in dan sanda da ke gadin wani banki ya gamu da ajalin sa a hannun wani dan’uwan sa, yayin da su ke shirin cin abincin rana a harabar bankin.

Wata Majiya ta ce, lamarin ya faru da ɗan sandan mai muƙamin kofur ne, lokacin da ɗan sandan ke wanke cokulan da za su ci abinci bayan ya bar bindigar sa a kan benci, inda makashin nasa ya ɗauki bindigar ya matsa kunamar sosai ya ɗirka masa harbi.

Majiyar ta ce, a makon da ya gabata ne ɗan sandan ya gabatar da mutumin a matsayin ɗan’uwan sa ga jami’an bankin da ke birnin Yenagoa na Jihar Bayelsa.

Kakakin Rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Bayelsa SP Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin.