Home Labaru Ɗan Majalisa Ya Shiga Tsomomuwa Bayan Ya Watsa Bidiyon Gwamna Akeredolu

Ɗan Majalisa Ya Shiga Tsomomuwa Bayan Ya Watsa Bidiyon Gwamna Akeredolu

92
0

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokoki ta Jihar Ondo
Ogmolaseye Oluwale ya shiga tsomomuwa, bayan ya watsa
bidiyon Gwamna Akeredolu yanƙwane a gadon asibiti.

Dan majalisr dai ya watsa biyo bidiyon ne domin taya Akeredolu murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

A cikin bidiyon, an nuno Akeredolu a ƙyamushe a gadon asibiti, bayan ya shafe tsawon watanni biyu ba tare da an bayyana inda ya ke ba.

Wani Fitaccen lawya a jihar Ondo Kayode Ayelo, ya ce ba a kyauta wa Akeredolu ba da har aka watsa hoton sa rame a dandalin sada zumunta, domin an keta ma shi haddi.

Sai dai kuma Ɗan Majalisar ya ce ba da wata ɓoyayyar manufa ya watsa bidiyon ba, kawai ya watsa bidiyon ne saboda maganganu marasa daɗi da wasu ke yi a kan rashin lafiyar Gwamnan.

Leave a Reply