Home Labarai ‘Ƴan Sanda Sun Rufe Majalisar Dokokin Jihar Filato Kan Rikicin Shugabanci

‘Ƴan Sanda Sun Rufe Majalisar Dokokin Jihar Filato Kan Rikicin Shugabanci

3
0
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ta kama wani fasto bisa zargin sa da yin garkuwa da kan sa domin karɓar kuɗi a wajen mabiyan sa.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ta rufe zauren majalisar
dokoki ta jihar a kan rikicin shugabancin da ake ci-gaba da yi.

‘Yan sandan kwantar da tarzoma sun isa harabar majalisar ne da misalin karfe 5 na safiya su ka toshe hanyar shiga.

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga ‘yan sandan kawo yanzu, amma rahotanni sun ce hakan ba ya rasa nasaba da rikici tsakanin ‘yan majalisar a kan wanda zai shugabance ta.

Kawunan ‘yan majalisar dai ya rabu biyu, inda wasu ke ɓangaren kakakin majalisar na yanzu Yakubu Sanda, yayin da wasu ke goyon bayan kakakin majalisar da kotu ta maida a kan kujerar Ayuba Abok, wanda aka tuɓe a watan Oktoba na shekara ta 2021.