Home Home ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Huɗu A Bauchi

‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Huɗu A Bauchi

152
0
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi, ta tabbatar da kashe wasu mutane huɗu da ‘yan bindiga su ka yi a anguwar Gambari Sabon-Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi, ta tabbatar da kashe wasu mutane huɗu da ‘yan bindiga su ka yi a anguwar Gambari Sabon-Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar SP Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin, a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya NAN.

SP Ahmed Wakili, ya ce ‘yan bindigar sun afka wa anguwar ne da tsakar daren ranar Asabar da ta gabata, inda su ka yi garkuwa da mutum ɗaya.

Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Aminu Alhassan, ya bada umarnin a gudanar da bincike domin kama waɗanda ke da laifi.

Leave a Reply