Wasu da a ke zargin mayaƙan kungiyar Boko Haram ne sun kashe sama da mutane goma sha biyu tare da ƙona kimanin gidaje talatin a wasu jerin hare-hare da su ka kai a ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar Neja
Mazauna yankunan sun ce hare-haren sun faru ne a tsawon makon da ya gabata, a garuruwan Alawa da Bangajiya da sauran su, inda baya ga kashe mutane da dama da maharan su ka yi sun kuma yi awon gaba da dukiya mai ɗimbin yawa.
Wani Mazaunin garin ya shaida cewa sama da makonni biyu ke nan su ke fama da tashe tashen hankula na hare-haren ƴan bindiga waɗanda su ka hana su sukuni a yankin.
A cewar sa, a makon da ya gabata ne ƴan bindigar su ka dasa bam a hanya wanda ya tashi da wasu da ke kan hanyar komawa ƙauyukansu daga kasuwa kuma nan ta ke mutane aƙalla takwas su ka rasa rayukansu.
Da a ka je kwashe gawawwakin waɗanda a ka kashe kuma a ka sake kai wani harin da ya yi sanadiyar asarar rayuka sannan su ka hana daukar gawawwakin wanda har ya zuwa yanzu babu labarin kwashe su.
A nashi bangaren, Shugaban ƙaramar Hukumar Shiroro Akiku Kuta ya tabbatar da harin.