Home Home Ƙungiyar Motocin Dakon Mai Na Nijeriya Ta Fara Yajin Aiki ‘Kan Tsadar...

Ƙungiyar Motocin Dakon Mai Na Nijeriya Ta Fara Yajin Aiki ‘Kan Tsadar Rayuwa’

139
0

Direbobin tankokin dakon man fetur a Nijeriya sun fara yajin aikin a ranar Litinin sakamakon ƙarin kudin da ake kashewa a wajen ayyuka, saboda faduwa warwas da darajar kudin Naira ya yi karo na biyu a cikin shekara guda da kuma yanayin hanyoyin kasar, in ji wani jami’in kungiyar.

Ƙungiyar masu tankokin dakon fetur ta Nijeriya NARTO, wadda ta haɗa dubban masu motoci da direbobin da ke da alhakin rarraba man fetur a ƙasar, na neman ƙarin kuɗin jigilar kayayyaki daga masu sayar da man saboda tashin farashinsa.

Ƙasar da ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziki a Afirka na fama da matsalar tsadar rayuwa, inda hauhawar farashin kayayyaki ta kai kusan kashi 30 cikin 100 a watan Janairu – mafi girma a kusan shekaru 30 da suka gabata, bayan da Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen tallafin man fetur, wanda ya kasance mai farin jini amma mai tsadar gaske, a watan Mayun da ya gabata tare da ɗage takunkumin da aka sanya a kan cinikin kuɗaɗen waje.

An fara samun dogwayen layukan man fetur a Legas, babban birnin kasuwancin Nijeriya, yayin da tasirin yajin aikin ya fara ƙamari.

Leave a Reply