Jam’iyyar PDP ta ce ƙarin farashin man fetur da aka samu a
Nijeriya wanda ya kai naira 617 a kan lita ɗaya rashin tausayi
ne da ake nuna wa ‘yan Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ta na ƙasa Debo Ologunagba, PDP ta ce bai kamata a riƙa saida litar man fetur a farashin da ya zarce naira 150 a Nijeriya ba.
Sanarwar, ta zargi gwamnatin tarayya da gaza warware matsalar tattalin arziƙin da ake fama da ita, da kuma ƙoƙarin tsawwala wa jama’a.
Masana harkar man fetur dai sun ta’allaka batun a kan ƙarin farashin gangar ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma faɗuwar darajar naira.