A ranar Talata da dare ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da yi wa
ma’aikatanta ƙarin kashi 25 zuwa 35 na albashinsu; ’yan fansho
kuma kashi 20 zuwa 28.
Sanarwar da Mai magana da Yawun Hukumar Kula da Albashi ta Kasa (NSIWC), Emmanuel Njoku ya fitar ta ce ƙarin zai fara
aiki ne daga watan Janairun 2024.
A saƙon Shugaba Tinubu, wanda ya fitar ta hannun Kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya ce ba wai kawai albashin ma’aikata ya kamata
a inganta ba, har ma da kayan aiki. Sai dai, Kungiyar NLC ta bakin Mataimakin Sakatarenta, Chris Onyeka, ya ce ƙarin albashin da aka yi bata lokaci ne kawai domin hukumar ba ta da hurumin kayyade mafi karancin albashi
na kasa.
NLC da sauran kungiyoyin kwadago dai na kiran a sanya mafi karancin albashi ya zama wanda zai wadaci ma’aikaci,
gwargwadon yanayin tsadar rayuwa a kasar nan.
Sun ce idan za a sa mafi ƙarancin albashi, dole a yi la’akari da yadda farashin kayan masarufi suke tashi, musamman bayan janye tallafin mai da gwamnatin ta yi.