Home Labarai Ƙarancin Kuɗaɗe: Emefiele Maƙetaci Ne, Macuci, Kuma Mamugunci – Soyinka

Ƙarancin Kuɗaɗe: Emefiele Maƙetaci Ne, Macuci, Kuma Mamugunci – Soyinka

3
0

Farfesa Wole Soyinka, ya zargi Gwamnan Babban Bankin
Nijeriya Godwin Emefiele da laifin cin zarafi da ƙuntata wa
ɗan Adam, wanda ya ce gagarumin laifi ne a duniya.

Ya ce Emefiele ya jefa rayuwar ‘yan Nieriya cikin ƙunci da talauci da wulaƙanci da tsananin wahala, sakamakon ƙarancin a hannun jama’a da ya ƙaƙaba da sunan sauya fasalin kuɗi.

Wole Soyinka ya bayyana haka ne, yayin tattaunawar da Gidan Talabijin na Channels ya yi da shi, inda ya ɗora laifin a kan Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya tsaya wa Emefiele ya haifar da masifa a cikin ƙasa.

Farfesan ya cigaba da cewa, Emefiele ya wulaƙanta ɗan Adam ta hanyar jefa shi cikin tozarci da ƙaƙa-ni-ka-yin yadda za su ciyar da kai da iyalai, ya na mai bayyana Emefiele a matsayin macuci kuma maƙetaci mamugunci.