gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda suka ce gwamnatin tarayyar na nuna musu wariya,
A ayyukan cigaba da gwamnatin tarayya ke yi, musamman tituna da layin dogo da suka haɗa yankin da sassan ƙasa.
Gwamnonin sun haɗa da jihar Adamawa, Bauchi, Borno, Taraba da kuma Yobe, sun gudanar da taron ƙungiyar karo na 10.
Shuwagabannin sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dubi yankin su wajen samar da waɗannan abubuwan more rayuwa.
Gwamnonin sun kuma nuna rashin jin daɗin su kan matsalar rashin wutar lantarki,
Ga kuma yadda kamfanin dakon lantarki na ƙasa TCN ke nuna halin ko’in kula game da batun.
Gwmanonin sun yaba da irin hadin kan da suka ba juna wajen ciyar da yankin su gaba a fannoni daban-daban.














































